Dan majalisar jihar Ebonyi ya raba irin shinkafa, N70m ga manoma

Dan majalisar jihar Ebonyi ya raba irin shinkafa, N70m ga manoma

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ikwo/Ezza ta kudu a majalisar wakilai ta tarayya, Chinedu Ogah ya raba buhunan shinkafa 25kg 200 tare da raba naira miliyan 70 ga manoman mazabar.

Dan majalisar wanda ya bayyana noma a matsayin mafita ga yunwa da wahalhalun da ke addabar kasar, ya bukaci jama’a da su shiga noma domin tsira da rayukansu da kuma magance yunwa da kuma samar da wadataccen abinci.

Ya kuma bayyana cewa rabon irin shinkafa da tallafin kudi ga manoman karkara shine don inganta harkar noma a mazabar sa.

Ogah wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar mai kula da cibiyoyi masu gyara, ya gargadi manoman kan cin iri

” Ina so in gode wa shugaban kasa da ya ba mu damar kawo ribar dimokuradiyya ga al’ummarmu. Hakan dai na nuna goyon baya ne ga kyakkyawan shugabanci na gwamnan jihar Francis Nwifuru. Na gode da yarda da ni.

Bari in yi gargadi, kar a dafa shinkafar nan, ba ta da kyau a ci, kai tsaye zuwa gona. Idan kun ci kuma kuna da matsala kada ku kira sunana”, ya yi gargadin.

Amma Gwamna Francis Nwifuru, wanda ya samu wakilcin Ofoke Kiran mai taimaka masa na musamman kan harkokin noma, ya bukaci wadanda suka amfana da su shiga aikin noma domin bunkasa wadatar abinci a jihar.